Labarai
Majalisar dokokiN Kano ta gayyaci Engr. Yusuf Bello Aliyu kan zargin cin zarafin Gwamna

Majalisar dokokin Kano ta gayyaci wakilin karamar hukumar Nassarawa, Engr. Yusuf Bello Aliyu, da ya gurfana a gaban kwamitinta na ladabtarwa na a gobe Talata, bisa zarginsa da cin zarafin Gwamnan Abba Kabir Yusuf.
A zaman majalisar na yau Litinin bisa jagorancin shugaban zauren Jibril Ismail Falgore, ta karɓi ƙudirin gaggawa daga wakilin karamar hukumar Minjibir, Abdulhamid Abdul, inda ya bayyana cewa, ya ga Bidiyon ɗan majalisar riƙe da kunnuwan Zomo a shafin Facebook tare da alaƙanta shi da Gwamnan Kano.
Abdul Minjibir ya ce, a matsayin su na masu doka, abun takaici ne ganin ɗan majalisa da ke wakiltar al’umma na amfani da kafafen sada zumunta ya na cin zarafin mutane da sunan siyasa.
Kudurin dai, ya samu goyon bayan ɗan majalisar Takai, Musa Ali Kachako, inda ya bayar da shawara kan samar da doka da za ta riƙa lura da kafafen sada zumunta.
Shima Shugaban marasa rinjaye na majalisar Usman Tasiu mai wakiltar Ƙiru, ya buƙaci kwamitin da ya gudanar da bincike na adalci kafin ɗaukar mataki.
You must be logged in to post a comment Login