Labarai
Majalisar dokokin Kano ta rage kwarya-kwaryan kasafin bana

Majalisar dokokin Kano ta gyara tare da rage kwarya-kwaryan kasafin kuɗin jihar, sakamakon sabuwar dokar haraji ta ƙasa.
Majalisar tayi gyaran dokar kasafin 2026 ne a zaman ta na yau Talata, bayan da Gwamnan Kano ya nemi a sake dubawa tare da gyara dokar.
Tun da fari kasafin kuɗin jihar a farkon shekarar 2026 ya kai Tiriliyan Ɗaya da Biliyan Ɗari huɗu da Arba’in da Bakwai, inda ya nemi a dawo da shi kasa zuwa Tiriliyan Ɗaya da Biliyan Ɗari Biyu da Ashirin da biyu.
Haka kuma a zaman majalisar na wannan rana ta amince da gyaran dokar kafa ƴan sandan jihohi.
Lawan Husaini Ceɗiyar ƴan gurasa, shugaban masu rinjaye na majalisar, ya bayyana irin gyare-gyaren da aka yiwa dokokin biyu.
You must be logged in to post a comment Login