Labarai
Wata mata ta yi barin cikin da ta ke dauke da shi a hannun yan Bindiga

Wata mata mai juna biyu da aka sace a gidanta da ke unguwar Alrahus Estate, Millennium City a jihar Kaduna, ta rasa cikin da take ɗauke da shi, bayan shafe makonni uku a hannun masu garkuwa da mutane.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an sace matar mai suna Jamila ne a ranar 6 ga watan Oktoba, tare da Abubakar Zakka, matarsa da kuma jaririyarsu mai watanni 6, lokacin da ’yan bindiga suka kai hari a gidansu da ke ƙaramar hukumar Chikun.
Wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar neman kuɓutar da su, ta ce masu garkuwar sun kira ta a ranar Talata, inda suka miƙa wayar ga Jamila, wadda ta bayyana cikin kuka cewa ta yi ɓarin cikin.
Majiyar ta ce duk da wannan mummunan lamari, ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da ita daga hannun masu garkuwar.
A baya, jaridar ta ruwaito cewa Abubakar Zakka, matarsa da jaririyarsu sun samu ’yanci kwanaki kaɗan bayan sace su, sakamakon yaɗuwar wani bidiyo a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna ɗan bindiga yana nufar kan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace da bindiga, yayin da jaririyar ke kuka.
Sai dai har yanzu wasu mazauna Millennium City da aka sace a wasu hare-hare daban-daban na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa.
You must be logged in to post a comment Login