Labarai
Akwai yiwuwar dage zaɓen 2027 idan cutar Ebola ta ci gaba da yaduwa- NCDC

Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasa , NCDC, ta ce akwai yiwuwar a dage babban zaɓen shekarar 2027 idan cutar Ebola ta ci gaba da yaduwa a fadin Najeriya.
Daraktan hukumar, Jide Idris, ne ya bayyana hakan, inda ya ce a halin yanzu babu buƙatar ɗaukar matakin dage zaɓen, amma idan cutar ta yaɗu sosai, gwamnati za ta iya duba yiwuwar hakan.
Idris ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, ida ya jaddada cewa jami’an lafiya ba za su yi amfani da cutar Ebola a matsayin makamin siyasa ba.
Ya ce hukumar na fatan zaɓen zai gudana kamar yadda aka tsara, inda ya ƙara da cewa za a iya la’akari da dage shi ne kawai idan cutar ta yaɗu sosai.
You must be logged in to post a comment Login