Labarai
Majalisar dokokin Kano ta rantsar da mambobi 2 da suka lashe zaɓe
Majalisar dokokin jihar Kano, ta rantsar da mambobinta biyu waɗanda suka sake samun nasarar a zaɓen cike gurbi a wasu mazaɓunsu.
Wakilan da aka rantsar a zaman majalisar na yau Litinin Muhammad Bello Butu-Butu wakilin Rimin Gado da Tofa, da takwaransa Zakariyya Alhassan Ishaq na Kura da Garun Malam, sun sha rantsuwar kama aiki ne daga Daraktan harkokin majalisar Barista Nasidi Aliyu.
Haka kuma bayan kammala rantsar da su din ne Muhammad Bello Butu-Butu, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar gabanin kotu ta ayyana zaɓensa a matsayin wanda bai kammalu ba, ya sake shan rantsuwa a matsayin shugaban Majalisar.
A baya dai kotun ɗaukaka ƙara ce ta ayyana zaɓukan mazaɓun Rimin Gado/Tofa sai Kura/Garun Malam, da kuma mazaɓar Ƙunci/Tsanyawa a matsayin waɗanda ba su kammalu ba,
Sai dai a yayin sake zaben hukumar INEC ta sanar da soke zaben Ƙunci/Tsanyawa sakamakon saɓa ƙa’idojin zaɓe.
You must be logged in to post a comment Login