Labarai
Majalisar dokokin Kano ta sahale gyaran dokar majalisar zartaswar Masarautu
Majalisar dokokin jihar Kano, ta amince da dokar gyaran majalisar zartaswar masarautun jihar ta shekarar 2019.
Majalisar ta amince da gyaran dokar ne tare da amincewa da yin amfani da taken jihar Kano yayin zamanta nay au karkashin jagorancin shugabanta Engr. Hamisu Ibrahim Chidari.
Haka kuma majalisar ta tattauna kan batun karbar kudaden tallafin rarrar manfetur daga gwamnatin tarayya wanda jihohi ke bin bashin shekaru hudu.
A wani labarin kuma, majalisar ta karbi wasika daga gwamna Ganduje da ya bukaci ta amince da Barista Mahmud Balarabe a matsayin cikakken shugaban hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
A ganawarsa da manema labarai, Shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari, ya yi karin haske kn batutuiwan da majalisar ta tattauna.
Danna Play domin sauraron muryar shugaban masu rinjayen
You must be logged in to post a comment Login