Labarai
Majalisar Kano ta buƙaci gwamnati ta umarci ƙananan hukumomi su riƙa raba abinci
Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta umarci ƙananan hukumomin jihar nan 44 da su riƙa ware Naira miliyan 25 duk wata domin sayan kayan abinci tare da raba su ga talakawa kyauta har na tsawon wata 7.
Majalisar ta buƙaci hakan ne a zamanta na yau Laraba biyo bayan ƙudurin gaggawa da ɗan majalisar Fagge a zauren Alhaji Tukur Muhammad ya gabatar.
Yayin gabatar da ƙuɗurin, ɗan majalisar na Fagge, ya ce, a halin yanzu al’umma na majalisar cikin halin kunci ta yadda har ma wasu ke yagar Tafasa domin sarrafa ta a matsayin abinci.
Da ya ke goyon bayan ƙudurin, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Madobi, Sulaiman Mukhtar Ishaq, ya ce, ƙudurin ya zo a lokacin da ya dace, tare da bayyana cewa ya kamata gwamnatocin ƙasar nan su gaggauta ɗaukar matakin sauƙaƙa wa al’umma wannan hali.
Ɗaukacin mambobin zauren, sun amince a kan gwamnatin ta yi amfani da hukumar CRC wajen gudanar da wannan aikin rabon kayan abinci.
You must be logged in to post a comment Login