Labarai
Majalisar Kano ta nemi Ganduje ya gina tituna a karamar hukumar Minjibir
Majalisar dokokin jihar Kano ta buƙaci gwamnatin Jihar Kano da ta gina titi a wasu hanyoyin da ke karamar hukumr Minjibir musamman hanyar da ta tashi daga garin Cheɗi ta bi ta Yola zuwa Ladin Ɗandake, ta haɗe da wata hanya da ke sada karamar hukumar, da hanyar da ke zuwa ƙaramar Ɓaɓura ta Jihar Jigawa.
Buƙatar hakan dai ta biyo bayan ƙudurin da dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Minjibir kuma mataimakin Shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Tasi’u Ibrahim Zabainawa ya gabatar a zaman majalisar na yau.
Alhaji Tasi’u Ibrahim Zabainawa ya ce al’ummar garuruwan na fama tarin matsaloli sakamakon rashin hanyar, duk kuwa da cewa akwai wata babbar kasuwa mai tsohon tarihi a yankin.
Da yake goyon bayan ƙudurin dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Sumaila Alhaji Zubairu Hamza Massu, ya ce ya kamata gwamnatin jiha ta yi gaggawar kaiwa al’ummar ƙaramar hukumar ɗauki.
Wakilinmu na majalisar dokokin ta Kano Auwal Hassan Fagge ya rawaito cewa bayan kammala zamanta na yau, majalisar ta ɗage ci gaba da zama har zuwa makon gobe.
You must be logged in to post a comment Login