Kiwon Lafiya
Majalisar koli kan tattalin arzikin ta kafa kwamiti don nemo mafita kan rikice-rikice
Majalisar koli kan tattalin arzikin Najeriya ta kafa wani kwamitin mutum goma domin nemo mafita kan rikice-rikice da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya a kasar nan.
Kwamitin wanda mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta yana kuma kunshe da gwamnoni tara.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce; sauran mambobin kwamitin sun hada da gwamnonin jihohin Zamfara da Kaduna da Adamawa da Benue da Taraba da Edo Da Filato da Ebonyi da kuma Oyo.
A cewar sa tuni kwamitin ya fara taron sa na farko jim kadan bayan sanar da sunayen mambobin sa.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kuma ce kwamitin ya sha alwashin gudanar da aiki tukuru domin samar da mafita kan rikicin da ake samu.
Tun da fari da ya ke karin haske kan taron majalisar kolin gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi, ya ce; mambobin kwamitin ba ya ga batun makiyaya sun kuma tattauna kan batun samar da kudade da za a rika samar da magunguna ga masu fama da cutar kanjamau.