Connect with us

Kiwon Lafiya

Shugaban Buhari ya karbi wasu shugabannin jam’iyyar APC a fadar Asorok

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi wasu shugabannin jam’iyyar APC a wajen wata liyafar cin abinci a fadar Asorok da ke Abuja a daren jiya.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Chief John Odigie Oyegun ne ya jagoranci ‘yayan jam’iyyar zuwa wajen liyafar cin abincin.

Sauran ‘yayan jam’iyyar ta APC da suka halarci liyafar cin abincin sun hada da: sakataren jam’iyyar Mai Mala Buni, da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Sokoto Aliyu Magatakarda Wamakko da tsohon gwamnan jihar Abia Uzor Orji Kalu da kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

Sauran sune: mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa Injiniya Segun Oni da tsohon gwamnan jihar Enugu Sullivan Chime da Olorogun O’tega Emerhor da tsohon gwamnan jihar Nassarawa Sanata Abdullahi Adamu da kuma Alhaji Abubakar Kawu Baraje.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,760 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!