Connect with us

Labarai

Majalisar Koli ta Shari’a ta kalubalanci matakin kafa ‘Yan-Sandan Jihohi

Published

on

Majalisar Koli ta Shari’a a kasar nan SCSN ta bayyana cewa duk da muhimmancin inganta tsaro, bai kamata a ɗauki kafa ‘Yan Sandan Jihohi a matsayin mafita kai tsaye ga matsalolin tsaron ƙasar ba.

 

Ta cikin warta sanarwar da Sakatare Janar na Majalisar, Nafiu Baba Ahmad,  ya fitar a ranar 30 ga Yulin 2026, majalisar ta ce matsalolin tsaro sun samo asali ne daga ƙarancin kuɗaɗe, cin hanci, ƙarancin jami’ai, rashin ingantattun kayan aiki, raunin tattara bayanan sirri da kuma rashin kyakkyawar haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.

 

Majalisar ta buƙaci a fara gyara da ƙarfafa hukumomin tsaron da ake da su, tare da nuna damuwa kan yadda ake gaggauta yin gyaran kundin tsarin mulki domin kafa ‘Yan Sandan Jihohi ba tare da cikakkiyar tattaunawa da ‘yan ƙasa ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!