Connect with us

Labarai

NLO ta sanar da ranar fara gasar matasa ‘yan ƙasa da shekaru 19

Published

on

Hukumar dake shirya gasar ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NLO) ta sanar da cewa za a fara gasar matasa ‘yan ƙasa da shekara 19 a ranar Asabar, 15 ga watan nan da muke ciki na Agusta.

 

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin sanarwar da ta fitar a shafukanta na Internet, inda ta ce an tanadi filayen wasa 16 da za su karɓi bakuncin gasar.

 

Hukumar ta NLO ta kuma sanar da cewa ranar Juma’a, 7 ga Agustan 2026 ce za ta kasance ranar ƙarshe ta rajistar ‘yan wasa, tare da umartar dukkan ƙungiyoyin da za su shiga gasar da su kammala rajistar ‘yan wasansu ta shafinta na yanar gizo.

Hukumar ta ƙara da cewa duk ƙungiyar da za ta fafata a gasar dole ne ta kasance tana da alaƙa da hukumar ƙwallon ƙafa ta jiharta, sannan ta biya kuɗin rajistar shekara-shekara da hukumar NLO ta kayyade.

 

Ta yi gargaɗin cewa duk ƙungiyar da ta kasa cika waɗannan sharuɗɗa za a ɗauke ta a matsayin wadda ta janye daga gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!