Connect with us

Labarai

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci a yi gaggawar kafa ‘yan sandan jihohi

Published

on

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen ceto dalibai da malamai da aka sace a jihohin Oyo da Borno, tare da sake jaddada bukatar kafa ’yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaro da ke addabar Nijeriya.

 

Jaridar Premium Times, ta rawaito cewa majalisar ta faɗi haka ne bayan tattauna wasu kudurori biyu da suka shafi sace-sacen dalibai da hare-haren da ake kai wa al’umma a sassan kasar nan.

 

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Ogbomoso ta Arewa da Ogbomoso ta Kudu a jihar Oyo, Hon. Olamijuwonlo Alao-Akala, ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-haren ’yan bindiga ke karuwa a yankunan Ogbomoso da Orire, yana mai cewa hakan ya zama babbar barazana ga rayuka da harkar ilimi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!