Labarai
Majalisar Tarayya ta gabatar da shawarar samar da ƙarin kujeru 74 na musamman ga mata

Majalisar tarayyar Najeriya, ta gabatar da shawarar samar da ƙarin kujeru 74 na musamman ga mata a Majalisar Dattawa da ta Wakilai, tare da tanadin kujeru uku ga mata a kowace Majalisar Dokokin Jiha, domin magance ƙarancin wakilcin mata a harkokin siyasar ƙasar.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ne ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin taron makon shari’a na shekarar 2026 da ƙungiyar lauyoyin mata ta duniya, reshen jihar Ekiti, ta shirya.
Sanata Bamidele, wanda ke wakiltar mazaɓar Ekiti ta Tsakiya, ya ce gyaran kundin tsarin mulkin da ake shirin yi na da nufin kawar da matsalolin da ke hana mata shiga harkokin shugabanci, tare da samar da tsarin siyasa mai bai wa kowa dama.
Ya ƙara da cewa shawarwarin na cikin aikin gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999 da ake gudanarwa, kuma za su samar da kujerun majalisa na musamman ga mata ba tare da cire ko maye gurbin waɗanda aka zaɓa a halin yanzu ba.
You must be logged in to post a comment Login