Labarai
Hukumar KCPC ta kama ’yan kasuwar Singa da ake zargi da yunƙurin sauya wa’adin ƙarewar amfani da Madara

Hukumar kare haƙƙin masu sayan kayayyaki ta jihar Kano KCPC, tare da haɗin gwiwar shugabancin kasuwar Singer, sun kama wasu ’yan kasuwa bisa zargin su da yunƙurin sauya wa’adin ƙarewar amfani da wata madara da wa’adinta ya riga ya ƙare.
Hukumar ta ce, ta kuma rufe shagunan da aka kama mutanen, bayan samun kiran gaggawa daga Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar, Aminu Umar Dogara, wanda ya sanar da ita wurin da ake gudanar da wannan aika-aika.
Daraktan sashen kula da ayyuka na hukumar, Alhaji Auwalu A. Muhammad, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a daren jiya Litini, ya ce KCPC na ƙoƙarin tabbatar da cewa ’yan kasuwa ba sa sayar da kayayyakin da wa’adin amfani da su ya ƙare ko waɗanda aka sauya musu bayanai ta hanyar da ta saɓa wa doka.
A nasa ɓangaren, Sakataren Zartarwar hukumar, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, ya ce ba za su zuba ido a na tauye haƙƙin masu sayen kayayyaki ba, ya na mai cewa duk wanda aka samu da irin wannan laifi, za a gurfanar da shi a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci.
You must be logged in to post a comment Login