Labarai
Atiku ya zargi shugaba Tinubu da gaza cika alƙawuran da ya yi na samar da wutar lantarki

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen badi da ke tafe Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gaza cika alƙawarin da ya ɗauka na samar wa al’ummar kasar nan wutar lantarki mai ɗorewa.
Atiku ya kuma yi alƙawarin kawar da tsarin farashin wutar lantarki mai matakai biyar, watau Bands tare da maye gurbinsa da wani tsari da ya ce, zai kasance mai adalci da gaskiya da kuma araha ga masu amfani da wutar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce, duk da manufofin gwamnatin tarayya da kuma kuɗaɗen da ta ke kashewa a fannin wutar lantarki, har yanzu ’yan Najeriya na fama da rashin ingantaccen hasken lantarki.
Ya kuma soki tsarin da ke raba masu amfani da wutar zuwa matakai A, B, C, D da E, ya na mai cewa wasu masu amfani da matakin A na biyan kusan naira ɗari biyu da tara da kwabo hamsin kan kowane unit kafin harajin VAT, duk da rashin tabbas kan samun wutar.
You must be logged in to post a comment Login