Labarai
Majalisar wakilai ta buƙaci a katse layukan sadarwa a Sokoto
Majalisar wakilan kasar nan ta yi kira ga hukumar sadarwa NCC da ta dakatar da ayyukan sadarwa a jihar Sakoto.
Majalisar ta buƙaci NCC din da ta rufe ayyukan sadarwa a wasu Kananan hukumomin da suka hadar da Bodinga, Dange-Shuni, da Tureta a Jihar Sakoto saboda rashin tsaro.
Majalisar ta kuma yi kira ga sojoji da su tura jami’an su zuwa sansanonin da abin ya shafa don dakile ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka a yankin.
Wannan dai ya biyo bayan kudurin da dan majalisa mai wakiltar Bodinga Dange-Shuni Tureta, Balarabe Kakale ya gabatar.
Kakale ya ce, an samu karuwar tabarbarewar yanayin tsaro a kananan hukumomi uku na mazabarsa a cikin makwannin da suka gabata, kuma hakan ya haifar da kisan gilla ga al’ummar yankunan Galma, Dutse, Buolere, da Hausare a gundumar wababe.
You must be logged in to post a comment Login