Labarai
Majalisar wakilai ta gayyaci ministan ilimi kan rufe makarantu
Majalisar dokoki ta kasa ta gayyaci Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu da ya zo ya yi ma ta jawabi kan dakatar da shirin bude makarantu da gwamnatin tarayya ta yi.
Shugaban kwamitin ilimi na majalisar, Alhaji Aminu Sulaiman Goro ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Freedom Radio.
Ya ce, ma’aikatar ilimi ta kasa ta sanar da su a baya, cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen bude makarantu ga daliban dake shirin shiga mataki na gaba, kuma ba su kara samun wani bayani ba, sai sanarwa kawai su ka ji daga Ministan ilimi cewa gwamanatin tarayya ta dakatar da shirin bude makarantun ba tare da an tuntube su ba.
Aminu Goro ya ce, hakan abun takaici ne, wanda ke nuna rashin hadin kan da ake samu tsakanin majalisar wakilai da kuma bangaren zartarwa.
You must be logged in to post a comment Login