Labarai
Majalisar zartaswa ta sahalewa hukumar Kwastam wajen siyo kayayyakin aiki
Majalisar zartaswa ta kasa ta amincewa hukumar yaki da fasakwauri ta kasa kwastam da ta kashe naira biliyan dari biyu da tamanin da uku da miliyan dari biyu da hamsin da biyar don sayo wasu kayayyakin aiki.
Ministan kudi kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad ce ta bayyana haka yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa wanda shugaba Buhari ya jagoranta jiya a Abuja.
Haka zalika Zainab Ahmed ta ce majalisar ta kuma sahalewa wani kwantiragi na daban a hukumar kula da shige da fice ta kasa wanda kudinsa ya kai sama da dala miliyan goma sha takwas.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren ta kara da cewa daya daga cikin kwantiragin an amince da shine tun a shekarar dubu biyu da goma sha takwas, sai dai a fitar da kudin yinsa ba, wanda za a sayi na’urorin binciken kwantainoni a tashoshin jiragen ruwa na Onne da ke fatakwal a jihar Rivers da kuma na Tin Can da ke Lagos.
A cewar ministan za a kuma sayo jiragen kwale-kwale guda goma ga hukumar yaki da fasakwauri ta kasa.
You must be logged in to post a comment Login