Labarai
Malam Abduljabbar Kabara ya dakatar da lauyansa
Malam Abduljabbar Shiek Nasir Kabara, ya dakatar da lauyan da yake kare shi a kotun ɗaukaka ƙara.
Yayin zaman Kotun na yau Laraba ƙarkashin jagorancin Mai shari’a Nasir Saminu, an gabatar da takardar dakatar da lauyan wadda Malamin ya sanya wa hannu a ranar 10 ga wannan watan da muke ciki na Mayu.
Sai dai lauyoyin gwamnati sun nemi kotu ta kori neman, tare kuma da buƙatar gyara a kan bayanan da kotun baya ta yi amfani da su wajen yanke masa hukuncin kisa.
Sai dai, kotun ba ta karɓi rokon lauyoyin gwamnati ba.
You must be logged in to post a comment Login