Labarai
Buhari ya bayyana damuwar sa kan karancin malamai a makarantun kasar nan
Gwamnatin tarayya ta ce malamai miliyan 1 da ake da su ba za su wadatar da adadin daliban kasar da yawansu ya kai sama da miliyan 42 ba.
Gwamnatin ta bayyana damuwarta game da karancin malamai a makarantun kasar nan, tana mai cewa akwai bukatar sake nazari akai
Shugaban hukumar bayar da ilimin bai-daya ta tarayya Dakta Hamid Boboye ne ya bayyana hakan lokacin da yake zagayen duba yadda jarrabawar tantance malamai ke gudana a birnin tarayya Abuja.
Ya ce, cikin malamai dubu 14 da suka rubuta jarrabawar a bana, malamai 3,700 ne za a dauka, wato za a dauki malamai dari-dari a ko wace Jiha sakamakon matsin tattalli arziki da ake fuskanta.
Dakta Hamid Boboye ya kuma ce akwai bukatar gwamnatocin Jihohi su tabbatar da ganin an ciyar da malaman da suka rubuta jarrabawar tantancewar gaba.
Har ma ya ce, hakan zai taimaka wajen samar da isassun malamai da za su wadatar da daliban kasar.
You must be logged in to post a comment Login