Ƙetare
Mamakon ruwan sama ya lalata gonaki da dama a birnin Damagaram

Rahotonni na nuni da cewar mamakon ruwan sama mai dauke da ƙanƙara da wasu yankunan jihar Damagaram na Jamhuriyyar Nijar ya fuskanta ya lalata tarin gonaki da ilahirin shukokin da aka yi.
Kafar yada labarai ta RFI ta rawaito cewa, a kalla garuruwa kusan 20 ne lamarin ya shafa a yankin na Damagaran.
Lamarin da ya jefa iyalai da dama cikin damuwa sakamakon asarar da suka tafka.
A cewar rahoton lamarin ya farune sakamakon ruwan saman da aka wuni ana yin sa a jiya Lahadi.
You must be logged in to post a comment Login