Connect with us

Labarai

Mambobi 70 na ACF sun bayyana goyon bayansu ga Bashir Dalhatu

Published

on

Fiye da mambobi 70 na Kwamitin Amintattu na kungiyar tuntuba ta Arewa wato ACF sun bayyana cikakken goyon bayansu gashugaban kwamitin, Bashir Dalhatu, tare da cewa babu wanda ya dakatar da shi daga shugabancin ƙungiyar.

 

Cikin wata sanarwa da wasu manyan jiga-jigan kungiyar suka sanya wa hannu, sun ce matakin da wasu tsirarun mambobi suka ɗauka na neman tsige Bashir Dalhatu ya saɓa wa kundin tsarin mulki da ƙa’idojin ƙungiyar.

 

Sanarwar ta kuma ce taron da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu ba halastacce ba ne, tare da zargin cewa an yi amfani da shi wajen yaɗa zarge-zarge marasa tushe kan shugaban kwamitin.

 

Daga cikin waɗanda suka sanya hannu a sanarwar akwai tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Yayale Ahmed, da tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, da kuma tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!