Labarai
Shalkwatar tsaro ta musanta kai wa fararen hula hari ta sama a Neja

Shalkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa fararen hula sun mutu a hari ta saman da sojoji suka kai a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Shalkwatar ta kuma bayyana cewa, harin ya faru ne a sansanonin ‘yan bindiga ne kawai.
A cewar daraktan yaɗa labaran ayyukan tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan.
Ya ce, an kai harin ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa, bayan taruwar ‘yan bindiga a ƙauyen Lukupe a ranar 9 ga Mayu, 2026.
Sojoji sun ce rundunar jiragen leƙen asiri ne suka kai hare-haren ta sama tsakanin karfe 11:59 na dare zuwa 6:00 na safe a wuraren da ake zargin maboyar ‘yan bindiga ne da suka haɗa da Katerma da Bokko da Kusasu da kuma Kuduru.
You must be logged in to post a comment Login