Connect with us

Labarai

Sojoji sun kashe jagoran yan ta’adda a Kogi

Published

on

Dakarun rundunar sojin Najeriya, sun kashe wani jagoran yan ta’adda a Jihar Kogi, bayan wani farmaki da suka kai a dajin Adankolo da ke Lokoja.

 

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi, ya fitar ranar Lahadi, ya ce, sojojin sun kai harin ne bayan samun ingantaccen bayanan sirri kan zirga-zirgar wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin.

 

Sanarwar ta ce sojojin sun yi kwanton ɓauna a hanyar da ake zargin ‘yan bindigar ke bi, inda aka yi musayar wuta. A yayin artabun, an kashe mutum guda daga cikin waɗanda ake zargi, yayin da sauran suka tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga.

 

Sojojin sun kuma kwato bindigogi biyu ƙirar AK-47 da harsasai guda 145, da ababen hawa da kuma kudade da suka kai Naira N62,900.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!