Connect with us

Labarai

NASWDEN ta umurci mambobinta su fara yajin aikin

Published

on

Ƙungiyar ƴan Gwangwan da ke harkar ƙarafuna da sarrafa shara ta ƙasa NASWDEN, ta umurci mambobinta a faɗin Najeriya da su fara gudanar da yajin aikin hulɗa da kamfanoni daga ranar 1 ga Oktoban 2026.

 

Ƙungiyar ta ce za ta dakatar da samar da karafa ga kamfanonin da ke sarrafa ƙarfe da ƙera rodika da sauran kayayyakin ƙarfe, a matsayin matakin nuna rashin amincewa da wasu matsaloli da ta ce suna, addabar kasuwancin nasu.

 

Mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Aminu Hassan Soja, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, ya na mai cewa, daga cikin matsalolin akwai zargin rage farashin karafa ba tare da sanar da su ba, da kuma cire wasu kuɗaɗe da ake kira “extra dust”.

 

Haka kuma ƙungiyar ta NASWDEN ta ce, yajin aikin zai fara ne daga ranar 1 zuwa 15 ga Oktoba, amma za a iya tsawaita shi idan ba a cimma yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanonin ƙarafan ba.

 

Sanarwar ta kuma ce, irin wannan sauyin farashi na iya janyo wa ƴan kasuwa asarar da ta kai tsakanin Naira miliyan uku zuwa shida kan duk mota guda.

 

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan zargin ƙarin shigar ƴan ƙasashen waje cikin harkar, da kuma sayen karafa daga dillalai da ba su da rijista.

 

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, shugaban ƙungiyar NASWDEN, Alhaji Abdulfatah Adisa Ogunwale, ya umarci mambobin ƙungiyar da su gudanar da yajin aikin cikin lumana, tare da bin doka da oda, da guje wa tashin hankali ko lalata dukiya.

 

Ƙungiyar ta ce, ta na fatan warware matsalolin ta hanyar tattaunawa da kamfanonin sarrafa ƙarafa da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Ƙungiyar ta ce tana fatan warware matsalolin ta hanyar tattaunawa da kamfanonin ƙarfe da sauran masu ruwa da tsaki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!