Connect with us

Labarai

Mambobin ISWAP 6 da iyalansu sun miƙa wuya ga sojoji

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta ce, mutane shida da ake zargin yan ƙungiyar tada ƙayar baya na ISWAP ne, tare da iyalansu, sun miƙa wuya ga dakarun rundunar Operation Hadin Kai a ƙaramar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.

 

Mukaddashin jami’in yaɗa bayanan rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya yi bayani kan nasarorin baya-bayan nan da rundunar ta samu a ayyukanta.

 

Ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen sun tsere ne daga maɓoyar mayaƙan da ke Guduf Bubayagwa da Chikide a tsaunukan Mandara da ke ƙaramar hukumar Gwoza.

 

A wani ci gaba kuma, Laftanar Kanar Goni ya ce dakarun Bataliya ta 115 da ke aiki a ƙaramar hukumar Askira-Uba sun kuɓutar da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su, yayin wani samame da suka kai maboyar ‘yan ta’adda a ranar 7 ga Yuli, 2026.

 

Ya ƙara da cewa an kai waɗanda aka ceto wani wuri mai tsaro, inda ake ba su kulawar likitoci da kuma tallafin da zai taimaka musu wajen murmurewa daga abin da suka fuskanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!