Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta ladabtar da wasu jami’an lafiya bisa sakaci da aiki

Published

on

Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta jihar Kano, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya ɗauki matakan ladabtarwa kan wasu ma’aikatan cibiyoyin lafiya da suka yi sakaci, tare da yabawa waɗanda suka nuna ƙwazo a bakin aiki.

 

Matakin ya biyo bayan ziyarar ba-zata da ya kai cibiyoyin lafiya na Tsalle da Gofaro a ƙaramar hukumar Gezawa da kuma Panshekara a Kumbotso domin duba yadda ake gudanar da ayyukan lafiya.

 

A cibiyoyin Tsalle da Gofaro, Daraktan ya sauke shugabannin cibiyoyin daga muƙamansu saboda rashin kulawa da yawan rashin zuwa aiki da aka samu, sannan ya ba da umarnin dakatar da albashin ma’aikatan da ba su halarci aiki ba har sai an kammala bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!