Connect with us

Labarai

Mazauna Dorayi sun nemi daukin mahukunta kan matsalar ambaliya

Published

on

Mazauna unguwar Dorayi bayan gidan Sarkin Dutse sun koka kan matsalar ambaliyar Ruwa a a yankin, tare da neman daukin mahukunta.

 

Hakan na cikin wata sanarwa da kungiyar gamayyar gazauna mazauna yankin suka fitar mai dauke da sa hannun Dakta Yusif Ibrahim.

 

Sanarwar ta ce sama da shekaru ashirin matsalar ke haifar musu da matsananciyar ambaliyar ruwa idan anyi ruwan Sama, sakamakon ƙarancin magudanar ruwa a yankin.

 

A cewar su matsalar ta haddasa musu asarar rayuka da dukiyoyi hadi da lalacewar gidaje da hanyoyi, tare da jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

 

A sabo da haka ne ta cikin sanarwar suke, kira ga Gwamnatin Kano da shugabannin yankin na Dorayi da hukumar REMASAB da sauran hukumomi kan su kai musu dauki.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!