Kasuwanci
Mambobin Majalisar Dokokin Kano za su yi wa Ɗan Adaidaita Sahu karo-karon kuɗi
Mambobin majalisar dokokin jiha Kano su 40 za su yi karo-karon kuɗi cikin albashinsu domin bai wa matashin nan mai sana’ar Tuƙa babur ɗin Adaidaita Sahu Auwalu Salisu da aka fi sani da Ɗanbaba, wanda ya tsinci kuɗi kimanin naira miliyan 18 a nan Kano tare da mayar da su ga mamallakinsu.
Shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar na yau Litinin, biyo bayan ƙudurin ƙashin kai watau Motion of Personal Explanation da ɗan Majalisar Doguwa Alhaji Salisu Ibrahim Muhammad ya gabatar.
Da ya ke gabatar da ƙudurin, ɗan majalisa na Doguwa, ya buƙaci majalisar har ma da ƙungiyoyin kishin al’umma da masu rajin tabbatar da aikata gaskiya da su karrama wannan matashi mai shekaru 21 da ya yi abun a taɓa duk da irin matsananci hali da suke ciki a gidan su.
Da ya ke mayar da martani kan abun a yaba da matashin ya nuna, shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore, ya bayyana cewa majalisar za ta gayyaci Ɗanbaba inda zai yi musabaha da shi tare da yin karo-karo don tallafa masa.
Ɗaukacin mambobin majalisar sun amince da ƙudurin tare da taba wa matashin wanda rahotonni suka tabbatar da cewa tun da jimawa ya daina zuwa makarantar Sakandaren Kawaji da ke yankin ƙaramar hukumar Nassarawa.
You must be logged in to post a comment Login