Labaran Wasanni
Manchester Uinted na kokarin daukar dan wasa Grealish
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta tattauna da kungiyar Aston Villa a wani kokari na neman cimma yarjejeniya kan dan wasan ta Jack Grealish.
United dai ta dade ta na zawarcin Jack Grealish mai shekaru 24 dan kasar Ingila, yayin da kungiyar ke ci gaba da neman mallakar dan wasan a yanzu.
A nan kuma, Tottenham Hotspur na kokarin lalata yunkurin kungiyar Manchester United na zawarcin dan wasan kungiyar Ajax Donny van de Beek.
Donny van de Beek dan kasar Netherlands mai shekaru 23 dan wasan tsakiya ne a kungiyar ta Ajax, wanda a yanzu kungiyoyi ke ta kokarin zawarcin dan wasan.
You must be logged in to post a comment Login