Labaran Wasanni
Manchester United ta nada Ralf Rangnick a matsayin mai horar da kungiyar na riƙon kwarya

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, ta sanar da nada tsohon mai horar da tawagar Schalke 04, dan ƙasar Jamus (Germany) Ralf Rangnick, a matsayin mai horar da ƙungiyar na wucin gadi (Interim).
Mai shekaru 60, Rangnick zai jagoranci ƙungiyar na tsawon wata 06, a matsayin mai horar da ƙungiyar na wucin gadi zuwa watan Mayu na shekarar 2022, kamar yadda sanarwar da ƙungiyar ta fitar a shafinta na Internet.
A makon da ya gabata, rahotanni suka mamaye kafafen yada labarai na Ingila da Jamus, na cewar Rangnick ya cimma matsaya da tawagar ta United , na horar da ƙungiyar , da kuma yiwuwar aiki da ita a gaba bayan kammala wa’adin sa, a matsayin mai bada shawara.
You must be logged in to post a comment Login