Labaran Wasanni
Mane ba zai wakilci Senegal ba a gasar kofin Duniya Qatar 2022

Ƙasar Senegal ta tabbatar da cewa ɗan wasan ta na gaba Sadio Mane ba zai buga kofin Duniya ba.
Ta cikin sanarwar da ƙasar ta fitar a Alhamis 17, ga Nuwamba 2022 hukumar ƙwallon ƙasar tace hakan ya biyo bayan raunin da ɗan wasan ya samu a wasan ƙungiyar sa ta Bayern Munich.
Ɗan wasan ya janye daga cikin tawagar inda za’ayi masa tiyata a raunin da ya samu.
A baya ƙasar ta Senegal ta saka sunan sa a cikin tawagar ta daga cikin ‘yan wasan da zasu taka mata leda a gasar ta bana 2022.
You must be logged in to post a comment Login