Labaran Kano
Manema labarai suna da damar da za su iya canza komai a kasa – CDE
Cibiyar ci gaban al’umma da wayar da kai ta ce, manema labarai sune ke da kaso mai yawa na inganta yadda ake gudanar da shugabanci a kasa.
Shugaban cibiyar Ambasada Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin taron wuni daya da cibiyar ta shiryawa manema labarai a jihar Kano.
Ya kuma ja hankalin manema labarai da su kara jajir cewa a kan ayyukan su, musamman wajen fito da gaskiya.
A cewar sa idan dan jarida ya jajir ce zai samu duk abin da ya kamata.
Taron ya gudana a ranar Laraba 4 ga watan Disambar shekarar 2024.
You must be logged in to post a comment Login