Labarai
Manoma sun biya kaso 24 na bashin Anchor Borrowers da CBN ya ba su- IMF
Asusun bada lamuni na duniya IMF yace manoma sun biya kashi 24 cikin 100 na bashin da suka karba karkashin shirin Anchor Borrowers na Babban Bankin Kasa CBN.
Wannan na kunshe ne a cikin sabon rahoton kasa da kasa game da harkokin kudi mai taken ‘Nigeria: Selected Issues’.
Rahoton dai ya nuna cewa kashi 76 cikin 100 na rancen ba a biya asusun na IMF ba.
Tun a ranar 17 ga watan Nuwambar 2015 ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin na Anchor Borrowers domin kulla alaka tsakanin kamfanonin da ke sarrafa kayayyaki da kuma kananan manoma.
A cikin rahoton na IMF ya kuma ce bashi a fannin noma a Najeriya bai yi wani tasiri wajen habaka bangaren ba, sakamakon gaza bawa wadanda suka dace da akeyi yayin bayar da bashin.
Rahoton: Abdukadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login