Tsaro
Manyan hafsoshin tsaro sun isa Maiduguri domin aikin wanzar da zaman lafiya

Manyan hafsoshin tsaron kasar nan sun isa birnin Maiduguri, domin ƙara ɗaukar matakan da za su inganta tsaro a yankin Arewa maso Gabas, bayan da mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar da manyan hare-haren Bama-bamai a jihar.
Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar O.O. Oluyede, tare da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shuaibu, ne suka isa birnin a wani muhimmin aiki na tsaro.
Ziyarar tasu na zuwa ne bayan umarnin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar, inda ya buƙaci shugabannin tsaro su mayar da cibiyar tsarawa da gudanar da ayyukan tsaro zuwa Maiduguri.
Ana ganin wannan mataki a matsayin wani sabon yunƙuri na ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
You must be logged in to post a comment Login