Labarai
Marigayi Ibro ya cika shekaru 10 da rasuwa
A yau Talata ne marigayi Rabilu Musa Ibro ya cika shekaru goma da rasuwa.
An haifi Marigayi Rabilu Musa wanda aka fi saninsa da Dan Ibro ne a ranar 12 ga watan Disamban shekarar 1971, ya kuma rasu a ranar Laraba 10 ga watan Disamban shekarar 2014 yana da shekaru 43 a duniya, bayan da ya shafe shekaru 23 a harkokin fina-finai.
Marigayin dai fitaccen dan wasan barkwanci ne, mai daukar nauyin shirya fina-finai kuma mai bada umarni, kana ya kasance daga cikin wadanda suka kafa masana’antar Kannywood, kuma har ya koma ga mahaliccinsa ana damawa da shi.
Marigayin jarumin dai ya halarci makarantar firamaren Danlasan lokacin yankin na karkashin karamar hukumar Wudil, daga nan ne kuma ya shiga makarantar Sakandire ta Government Teachers College Wudil, daga bisani ya samu nasarar kammala karatunsa na NCE.
Haka kuma marigayi Rabilu Musa Ibro ya shiga aikin hukumar gidan gyaran hali lokacin ana kiranta da gidan yari watau Nigerian Prison Service a shekarar 1991 bayan wasu shekaru kuma ya ajiye aikin ya tsunduma harkokin wasan kwaikwayo inda ya fara yin fim mai suna ‘Yar Mai Ganye.
Rabilu Musa Dan Ibro ya lashe kyautuka da dama da suka hadar da kyautar Nigeria Entertainment Awards a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2014 da kyautar Kannywood and MTN Awards ta shekarar2015 da sauransu.
Sai dai har a yanzu da marigayin ya shafe shekaru 10 da rasuwa, Wasu mazauna birnin Kano, na ci gaba da bayyana alhininsu game da rasuwar marigayin.
Freedom Radio, ta tattauna da uwar gida ga Marigayi Ibro Hajiya Jimmala, wadda ta shaida mana irin yadda suka gudanar da rayuwar aure da shi.
Ta ce, sun gudanar da rayuwar zaman aure cike da zaman lafiya da walwala, don kuwa ba su cika samun sabani da shi ba, haka kuma ko da sun samu sabanin ma za su shirya ba tare da bata lokaci ba.
Hajiya Jummala, ta kara da cewa, sai dai bayan rasuwar marigayi Ibro kawo yanzu babu wasu abokan sana’arsa da ke tallafa mata illa dai ‘yan uwanta.
A tattaunawar Freedom Radio da Malam Mansur Sani Sharada da aka fi sani da Malam Kwaram wanda ya kasance amini ga marigayi Ibro, ya bayyana cewa sun shaku da juna don kuwa alakarsu ta samo asali ne tun a makarantar Sakandare horas da malamai ta GTC Wudil.
“A gabana marigayi Ibro ya rasu, saboda na je asibiti duba shi ranar Talata kamar yadda na saba, amma sai na ga jikinsa ya yi zafi a ranar, saboda haka sai na kasa tafiya ni ma na kwabna a asibitin, amma washe gari Laraba da Asubah Allah ya yi masa cikawa” a cewar Malam Kwaram.
Kafin rasuwarsa dai ya fito a fina-finai da dama da suka hadar da ‘Yar mai Ganye da Ibro Awilo da Dan Malam da Allo da Ibro A Makka da sauransu.
Marigayi Rabilu Musa Ibro dai ya rasu ya bar matan aure 4 wadanda suka hadar da Jamila da Talatu da Ummi Da kuma Kubura, kuma ya bar ‘ya’ya 19 a duniya.
Da fatan Allah ya kyauta makwancinsa da namu baki daya
You must be logged in to post a comment Login