Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Tarihi da Al'adu

Marigayi Sani Abacha ya cika shekaru 21 da rasuwa

Published

on

A yau Asabar 8 ga Yunin 2019 ne marigayi tsohon shugaban Najeriya na mulkin Soja marigayi Janar Sani Abacha ya cika shekaru 21 da rasuwa.

An dai haifi marigayi Janar Sani Abacha a jihar Kano a shekarar 1943, wanda ya rasu a rana irin ta yau a shekarar 1998.

Marigayin dai ya rasu ne yana matsayin shugaban kasa na mulkin Soja inda ya fara mulkin Nijeriya daga ranar 17 ga watan Nuwamban shekarar 1993 bayan da ya hambarar da gwamnatin Chief Ernest Shoneken.

Marigayi Sani Abacha wanda ya fara aikin soja tun daga karamin soja har ya kai matsayin Janar ba tare da ya tsallake ko da mukami daya ba, daga bisani ya bayyana sha’awar sat a mulkar kasar nan karkashin mulkin farar hula inda ya samu goyon bayan jam’iyyun siyasar wancan lokacin guda 5 wadanda suka hadar da jami’yyar UNCP da CNC da DPN da NCPN da kuma jam’iyyar GDM.

Duk da caccaka da sukar da gwamnatin tasa ta sha daga kungiyoyin kare ‘yancin Dan-adam na cikin kasar nan da ma na kasashen ketare sakamakon kamawa tare da tsare ‘yan siyasar da ke kalubalantar gwamnatin tasa, wadanda suka hadar da Chief Olusagun Obasanjo da Bola Ahmad Tunubu da Sanata Shehu Sani da tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da marigayi tsohon gwamnan Kano Alhaji Abubakar Rimi da marigayi Chief MKO Abiola da marigayi Shehu Musa ‘yar Adua Sai dai gwamnatin tasa ta samar da ayyukan raya kasa da suka hadar da kafa asusun rarar man fetur watau PTF wanda ya ta’allaka wajen yin ayyukan da suka shafi kula da makarantu da asibitoci da gina tituna.

Tsohon shugaban kasar ya kuma samar da karin jihohi 6 da suka kunshi jihar Bayelsa da Zamfara da Ekiti da Gombe da kuma jihar Nassarawa, tare da karin kananan hukumomi inda jihar Kano ma ta samu karin kananan hukumomi 10 kan 34 da take da su a baya.

Marigayi Sani Abacha dai ya rasu ne a fadar gwamnati dake Villa a birnin tarayya Abuja bayan ya shafe shekaru 5 yana gudanar da gwamnatin mulkin soji.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!