Labaran Kano
Marigayi mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero yana Kallan wasan kwaikwayon Hankaka
An bayyana marigayi mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero a matsayin daya daga cikin mashahuran mutanan dake kallan wasan kwaikwayo na hankaka.
Babban jarumin shirin Muhammad B Umar wanda aka fi sani da Hankaka ne ya bayyana haka a wata tsohuwar tattaunawa da muka yi da shi.
Hankaka ya shaida min cewa wani lokacin ko Marigayi Alhaji Ado Bayero bai samu kallan shirin ba ana aikowa domin a karbar masa kwafi.
Muhammad bin Umar Hankaka ya kara da cewa shima shararran malamin Addinin musuluncin nan kuma Marigayi Wazirin Kano Sheikh Isa Waziri yana daya daga cikin masu kallan shirin wasan kwaikwayon na Hankaka.
Shirin wasan kwaikwayo na Hankaka ana gabatar da shi ne a gidan Talabijin na ARTV wanda tun lokacin yana gidan talabijin na CTV 67.
Shirin wasan kwaikwayo na Hankaka ya yi shuhura sakamakon barkwanci dake cike da shirin da kuma nishadantarwa.
Shirin wasan kwaikwayon na Hankaka yayi tashe a shekarun 1990 har zuwa shekarun 2000.