Labarai
Masarautar Bichi ta nemi hadin kan kungiyoyi domin samar da Lantarki mai amfani da hasken Rana
Majalisar Masarautar Bichi, ta bukaci da ta hada hannu da kungiyoyi masu zaman kansu da nufin samar da wadataccen hasken wutar lantarki a wasu yankunan masarautar ta hanyar amfani da hasken rana.
Mai martaba sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero OFR, ne ya mika bukatar hakan lokacin da yake bude aikin tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kauyen ‘Yal’lami da ke yankin karamar hukumar Bichi.
tun da fari dai, Majalisar Masarautar ta Bichi da hadin gwiwa wani kamfani ne suka gudanar da ya aikin wanda ya lashe miliyoyin naira.
Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero OFR ya kara da cewa, tasha za ta samar da wutar da za ta taimaka wa al’umma matuka, don haka akwai bukatar sake samar da karin wata domin ci gaban al’umma.
You must be logged in to post a comment Login