Connect with us

Labarai

Masarautar Gaya ta hana Hakimai zaman Karaga a fadojinsu

Published

on

Masarautar Gaya ta hana hakimai zaman karaga a fadojin su tare da umartar waɗanda suke amfani da ita su gaggauta dena nan take.

 

Hakan na cikin sanarwar umarnin da Wamban Gaya kuma Babban Dan Majalisar Sarki, Dr. Mansur Ibrahim Gaya, ya fitar.

 

Sanarwar ta bayyana cewa bisa al’adun Masarautar Gaya, akwai wasu abubuwa da suka kebanta ga Sarki kaɗai, ciki har da kakaki, zaman karaga a fada, jiniya a mota da sauran al’adun masarauta.

 

Haka zalika ta ce dukkan hakiman da suke sanya karaga a fadojinsu su gaggauta cire ta, tare da daina amfani da ita.

 

Sanarwar ta buƙaci hakiman da su ci gaba da kiyaye ƙa’idoji da dokokin Masarautar ta Gaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!