Labarai
Sarkin Musulmi ya musanta rahoton goyon bayan sake zaɓar shugaba Tinubu a 2027

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya musanta rahoton da ke cewa ya bayyana goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.
Haka na kunshe cikin sanarwar da Prince Bashir Adefaka ya fitar a madadin Sashen Yaɗa Labaran Masarautar a daren jiya Talata.
Sanarwar ta bayyana cewa ba zai yiwu Sarkin Musulmi ya yi irin wannan furuci ba, domin a matsayinsa na uba ga kowa ba ya nuna bambanci tsakanin ‘yan siyasa ko jam’iyyun siyasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa Sarkin Musulmi na ci gaba da karɓar duk masu neman shawararsa da addu’arsa ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba, tare da buƙatar al’umma su yi watsi da rahoton da ke danganta shi da goyon bayan kowane ɗan takara.
Haka kuma sanarwar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su.
You must be logged in to post a comment Login