Labarai
Muhammadu Sanusi II na nan Daram a matsayin Sarki- Gwamna Abba

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II yana nan daram akan kujerarsa ta sarauta, yana mai cewa babu wani abu da zai same shi duk da ce-ce-ku-cen da ake ta yadawa dangane da masarautar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin ziyarar barka da Sallah da sarkin kano na 16 Khalifa Muhammadu Sunusi II ya kawo masa a fadar gwamnatin jihar a wani ɓangare na hawan Nassarawa da aka saba gudanarwa duk shekara, inda ya ce gwamnatin sa tana tafiyar da dukkan lamurra cikin hikima da lissafi domin tabbatar da zaman lafiya da mutuncin masarautar Kano.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin jihar Kano tana da cikakken yakini da shugabancin Khalifa Muhammadu Sunusi II, yana mai jaddada cewa duk wasu matakai da gwamnati ke ɗauka suna gudana ne bisa doka da tsarin da ya dace.
Ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan al’ummar jihar Kano za su shaida gudanar da hawan daba ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kano na 16 Khalifa Muhammadu Sunusi II, lamarin da ya ce zai ƙara tabbatar da martaba da ɗaukakar masarautar Kano.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ka iya haddasa rikici, tare da tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da kare martabar masarautar Kano da kuma tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.
You must be logged in to post a comment Login