Kiwon Lafiya
Masarautar Kano ta yi alkawarin shiga cikin al’amuran masu maganin gargajiya
Masarautar Kano ta yi alkawarin shiga cikin al’amuran masu maganin gargajiya da nufin tsabtace harkokin bangaren ta hanyar kakkabe miyagun kalamai da zantukan batsa da kauda bata gari a cikin sana’ar a fadin jihar Kano.
Jarman Kano Farfesa Isah Hashim ne ya bayyana hakan a yayin da ya karbi bakuncin kungiyar masu sana’ar maganin gargajiya a karkashin jagorancin shugaban ta na jiha Malam Ahmad Ali Kofar Na’isa a wata ziyara da suka kai fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu.
Farfesa Isah Hashim ya bayyana cewa al’umma sun damu matuka da irin kalaman da wasu daga cikin masu maganin gargajiya suke yi a yayin saida magunguna a cikin jihar nan, saboda akwai bukatar su kasance masu kiyayewa da dabi’u da al’adun da dokoki da kuma addinin mutanen Kano.
Da yake jawabi, shugaban kungiyar masu maganin gargajiya Malam Ahmad Ali Kofar Na’isa ya ce sun je fadar ne domin su nemi goyan baya da hadin kan masarautar kano a kokarin dakile llar da wasu masu sana’ar maganin gargajiya suke haifarwa a tsakanin al’umma.