Labarai
Masari ya sanya sabbin matakan gaggawa bakwai kan matsalar tsaro a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da ɗaukan wasu sabbin matakai domin magance matsalar tsaro da ke addabar jihar.
A ranar Litinin ne Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari, ya sanya hannu kan dokar sabbin matakan na gaggawa.
Mataki na farko shi ne, an rufe hanyar Jibiya zuwa Gurbin Baure, sai dai masu abin hawa su bi ta garin Funtua.
Na biyu kuma an rufe hanyar ƙanƙara zuwa Jibiya.
Na uku an hana manyan motoci ɗaukar ita ce a daji.
Mataki na huɗu an hana shigawa ko fita da dabbobi daga jihar.
Na biyar kuma shine Gwamnati ta haramta goyon mutane uku a kan Babur.
Mataki na shida kuwa shi ne, masu ƙananun motar ɗaukar fasinja kada su ɗauki sama da mutane uku.
Na bakwai shi ne, Gwamnatin ta Katsina ta hana zirga-zirga daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe.
Sai mataki na bakwai ta haramta sayar da man fetur a jarka a gidajen mai.
Sai dai an yi sassaucin wannan doka a kan ƴan jarida, da jami’an tsaro da kuma ma’aikatan lafiya.
Dokar zata far aiki daga ranar Talata 31 ga watan Agustan 2021.
You must be logged in to post a comment Login