Kiwon Lafiya
Masu ciwon sikari su rinka sahur da abinci mai nauyi-Likita
Wani kwararre likitan kula da masu cutar ciwon sikari Dr Ibrahim Dan-Jumai Kura ya bukaci masu cutar da su riga yin sahur da abinci mai nauyi don gujewa shiga matsala a yayin watan Ramaddan mai zuwa.
Dr Ibrahim Dan-Jumai Kura ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan gidan Radio Freedom, wanda ya maida hankali kan hanyoyin da masu wancan cutar za su bi don kiyaye lafiyar su.
A cewarsa, masu cutar Sikari su kuma riga yawaita shan ruwa duba da irin zafin da ake fama da shi a wannan lokacin.
Shi ma wani kwararren Likita a fanni abinci mai gina-jiki Malam Yusuf Salish Kura, ya ce yana da kyau mai azumi ya fara cin kayan itatuwa da zarar ya bude baki, daga bisani sai a sha abu mai dan-dumi-dumi don inganta lafiya.
Masanan dai sun bukaci al’ummar musulmai da su gujewa amfani da ruwa mai sanyi da kuma rage zama cikin sanyi sosai kare kare lafiya.
You must be logged in to post a comment Login