Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Mutum na farko ya rasu sakamakon Coronavirus a Kano

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce mutum na farko mai dauke da cutar Coronavirus ya rasu a jihar.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter da misalin karfe 11:55 na dare ta ce mutum na farko mai dauke da cutar Corona ya rasu.

Sanarwar ta kara da cewa an samu karin wadanda sakamakon gwajinsu ya nuna cewa suna dauke da kwayar cutar ta Coronavirus.

Izuwa yanzu hukumar tace mutane 21 ne ke dauke da cutar a jihar Kano.

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ta sanya dokar zaman gida ga al’ummar jihar domin dakile yaduwar cutar daga daren ranar Alhamis.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!