Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Masu cutar Corona 11,828 sun warke a Najeriya

Published

on

Cibiyar dakile bazuwar cutuka ta Najeriya NCDC ta ce mutum 11,828 sun warke daga cutar Corona a kasar.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da NCDC ta fitar a shafinta na Twitter, wanda ta ce a ranar Litinin an samu karin mutane 575 wadanda suka kamu da cutar a jihohi 19 na kasar, da kuma birnin tarayya Abuja.

NCDC ta ce zuwa yanzu mutum 29,286 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Corona a sassan kasar nan.

654 daga ciki cutar tayi ajalin su.

Hakan na nufin yanzu masu masu cutar Corona 16,804 ne su ka rage a Najeriya, wadanda ke cigaba da samun kulawa daga jami’an lafiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!