Labarai
Masu makarantu su bi ka’idoji kafin bude makarantu – Minista
Gwamnatin tarayya ta baiwa masu makarantu wa’adin zuwa ranar 29 ga wannan watan da su samar da dokoki da aka shinfida musu don samun kariya wajen bude makarantu a kasar nan.
Karamin ministan ilimi Emeka Nwajiuba ne ya sanar da hakan a ya yin da yake jawabi wajen taron kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar Corona a yau Juma’a.
Nwajiuba ya ce ana son makarantu su samar da dukkanin abunda ake bukata su samar da dukkanni abunad ake bukata su kai rahoto ga ma’aikatar ilimi na jihohin su nan da ranar 29 ga watan nan da muke ciki.
Ministan ya kara da cewar ma’aikatar ilimi ta hada hannu da ma’aikatar lafiya da cibiyar dakile cututtuka ta kasa NCDC don bin dokokin kan bude makarantu.
Akan haka ne gwamnatin tarayya ta nemi masu makarantu su bi dukkanin ka’idoji wajen bude makarantu a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login