Labarai
Mata nada rawar takawa a fanin Noma- SASAKAWA
Ƙungiyar bunƙasa noma ta Afrika SASAKAWA, ta bayyana cewa mata nada muhimmiyar rawa da za su taka wajen haɓɓaka harkokin noma a Najeriya.
Ƙungiyar ta bayyana hakan mlne ta cikin wata sanarwa da ta fitar mai alaƙa da Bikin ranar mata ta bana.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ƙungiyar Moses Nongoatse, ta ƙara da cewa SASAKAWA za ta tallafa wa mata musamman a bangaren harkokin noma har ma da sarrafa abinci.
Moses Nongoatse, ya kuma ce, majalisar dinkin duniya ce ta ƙirƙiri bikin ranar Mata ta duniya domin ya bawa mata akan irin rawar da suke takawa a fannoni da dama kamar kasuwanci da Al’adu da Siyasa da sauransu.
You must be logged in to post a comment Login